Masana tattalin arziki a Najeriya sun ce hasashen IMF a kan raguwar hauhawar farashin kaya a karshen 2024, a kasar shaci-fadi ne kawai
Wasu masana tattalin arziki a Najeriya sun ce hasashen da Asusun Lamuni na Duniya IMF ya yi cewa za a samu raguwar hauhawar farashin kaya a kasar a karshen bana, romon baka ne kawai.
Masanan sun ce wannan ba abu ne mai yiwuwa ba matukar ba a dauki matakan da suka kamata ba.
Cikin wata hira da ya yi da BBC, Dakta Murtala Abdullahi Kwara, shugaban sashen nazarin tattalin arziki na jami’ar Umaru Musa ‘Yar-Aduwa da ke Katsina, ya ce ko shakka babu hasashen da ya zo daga masana, to amma abin mamaki idan aka kalli wani abin to tabbas za a ga babu wani dalilin fadarsa sai don a farantawa wasu bangare na gwamnati rai ko kuma wasu sun yi rawa ya kamata a yaba musu.
Ya ce,” Idan aka yi la’akari da yadda farashin wasu manyan kaya ke tashi a kullum ya za a yi a gasgata hasashen IMF?”.
Masanin tattalin arzikin, ya ce, “Tun da farko ma hasashen Asusun Lamunin cewa ya yi farashin kaya ya tashi da kashi 33 cikin 100 a yanzu, to wannan ba gaskiya ba ne, sannan kuma ta ina za a yar da da cewa farashin zai sauka kashi 24 cikin 100 bayan ba a hakikance yadda farashin ma ke tashi.”
“ Matsaloli biyu a Najeriya na tashin farashin dala duk da yanzu gwamnati na kokarin daidaita bangaren da kuma tashin farashin mai, sune zasu sa duk wani hasashe da IMF zai yi muke kallonsa a matsayin shaci fadi ne kawai wanda bashi da wata makama.”In ji shi.
Dakta Murtala Abdullahi Kwara,ya ce duk wanda ke rayuwa a Najeriya ba sai na fada masa cewa matakan da gwamnatin kasar ke dauka na tattalin arziki, kara tsunduma talakan kasar cikin wahala suke.
Ya ce, “ Duk wani tsari da aka fito dashi a Najeriya wanda IMF ke bayar da shawara a kansu, wannene ya yi tasiri? Misali cire tallafin mai wanda shi ne ya haifar da bala’in da Najeriya ta tsinci kanta ciki a yanzu, haka tsare tsaren tsuke bakin aljihu da gwamnati ta fito da su me ya canja?”
Masanin tattalin arzikin ya ce idan aka bi tarihi babu wata kasa guda a duniya da ta bi shawarwarin IMF da yanzu ta ke zaune lafiya.
“Idan gwamnatin Najeriya ta na son a samu raguwar hauhawar farashin kaya a kasar ta ta fito ta yi tsarin da mutane za su samu mai cikin sauki, sannan a bangaren dala kuma, ya kamata gwamnati ta fito da wasu tsare tsare masu karfi na nan take da za a magance matsalar.” In ji shi.